Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta nemi masu zuba jari su saka hannu a fannin tsaftar muhalli

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga ‘yan kasuwa da masu zuba jari da su saka hannun jari a fannin tsaftar muhalli domin inganta lafiyar al’umma, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arziki.

 

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Kano kan yadda za a ƙarfafa rawar da masu zaman kansu za su taka wajen magance matsalolin tsaftar muhalli.

 

A cewarsa, gwamnatin jihar na kallon fannin tsaftar muhalli a matsayin wata dama ta kasuwanci, inda ya ce ana buƙatar saka hannun jari a gine-ginen bandakunan jama’a, sarrafa najasa da kuma cibiyoyin tace shara domin samar da wasu albarkatu.

 

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta fara aiwatar da wasu sauye-sauye da suka haɗa da ƙarfafa hukumomin kula da muhalli da kuma ƙaddamar da shirin Smart Kano Waste and Sanitation Initiative, wanda ke da nufin inganta ayyukan tsaftar muhalli da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.

 

Dakta Hashim ya yi kira ga masu zuba jari, cibiyoyin kuɗi da abokan hulɗar ci gaba da su tallafa wa ayyukan tsaftar muhalli masu ɗorewa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare lafiyar al’umma da samar da ƙarin ayyukan yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!