Connect with us

Labarai

Tsagin Wike ya magantu kan wallafa yan takarar PDP da INEC ta yi

Published

on

Bangaren jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce wallafa sunayen ‘yan takararsa na shugaban ƙasa da na majalisun dokoki da Hukumar INEC ta yi ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin babban zaɓen shekarar 2027.

 

A cikin wata sanarwa, sakataren yaɗa labarai na bangaren jam’iyyar, Jungudo Mohammed, ya ce bayyana sunayen Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da Babangida Umar a matsayin mataimakinsa ya ƙaryata iƙirarin da ake yi cewa PDP ba za ta tsayar da ɗan takara ba.

 

Mohammed ya kuma gode wa INEC, ɓangaren shari’a da hukumomin tsaro kan gudanar da aikinsu bisa doka. Ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da yunƙurin sasanta saɓani a cikin gida tare da maraba da tsofaffin da sababbin mambobin da suka shiga cikinta, yana mai cewa PDP na da burin samar wa ‘yan Najeriya ingantaccen shugabanci a zaɓen 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!