Connect with us

Labarai

Shugabannin PDP sun nemi Jonathan ya nesanta kansa da kalaman yan tsagin Turaki

Published

on

Shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi masu goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, sun buƙaci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya fito ya nesanta kansa daga abin da suka kira amfani da sunansa da tsagin Kabiru Turaki ke yi.

Da ya ke magana a Abuja, jagoran shugabannin PDP na jihohi, Austin Nwachukwu, ya ce amfani da sunan Jonathan na iya yin illa ga martabarsa da ta jam’iyyar. Ya kuma yi zargin cewa tsagin na Turaki ba shi ne halastaccen shugabancin PDP ba, tare da kira ga jam’iyyar ta ɗauki matakan shari’a kan lamarin.

Jam’iyyar PDP bangaren Turaki ta ayyana Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2027, duk da cewa tsohon shugaban bai halarci taron da aka yi a Abuja ba, kuma har yanzu bai yi wata sanarwa a bainar jama’a kan batun ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!