Labarai
Sojoji sun kama ƴan Boko Haram 4 a Jihar Yobe

Dakarun sojin Najeriya, sun kama mutane huɗu da ake zargin ƴan Boko Haram ne bayan wani kwanton ɓauna da suka yi a Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Ta cikin sanarwar da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Talata, ya ce Sojojin tare da Civilian Joint Task Force CJTF sun yi kwanton ɓaunar ne a gabashin Azare da misalin ƙarfe 11:00 na daren Litinin, 21 ga Satumba, inda suka yi artabu da waɗanda ake zargin ƴan ta’adda ne.
Bayan artabun, Sojojin sun kama mutane huɗu da ake zargin ƴan Boko Haram ne, tare da ƙwato kekuna huɗu, kayan abinci masu yawa, tinkiya ɗaya da harsasai.
Sanarwar ta ce mutanen da aka kama da kayayyakin da aka ƙwato suna hannun Sojoji domin ci gaba da bincike, yayin da ake ci gaba da faɗaɗa bincike a yankin.
You must be logged in to post a comment Login