Connect with us

Labarai

Gwarzo ya buƙaci Matasa da Mata su yi rajistar katin zaɓe kafin wa’adin INEC

Published

on

Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya buƙaci dukkan mutanen da suka cancanci yin rajistar katin zaɓe amma har yanzu ba su yi ba, musamman matasa da mata, da su yi amfani da sabon tsarin rajistar a shafin Internet na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC kafin wa’adin ranar 24 ga Yulin bana.

Aminu Abdussalam Gwarzo, ya buƙaci hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar.

Ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar NDC, ya bayyana cewa sabon shafin rajista na INEC ya na bai wa masu kada ƙuri’a karo na farko damar fara da kammala rajistarsu ne daga gida ta hanyar amfani da lambar NIN.

Ya ƙara da cewa, wannan tsari ya rage wahalar zuwa bin layuka masu tsawo domin yin rajista, ya na mai bayyana katin zaɓen a matsayin babbar hanyar kawo sauyi mai amfani ga dukkan al’umma.

Ya kuma yi kira musamman ga matasa da mata da su yi rajista, su kuma karɓi katunansu sannan su shirya domin amfani da haƙƙinsu na zaɓe a shekarar 2027.

Kwamared Aminu Abdussalamu Gwarzo, ya kuma buƙaci shugabannin al’umma, ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyin matasa da kungiyoyin farar hula da su taimaka wajen wayar da kan jama’a game da muhimmancin rajistar masu zaɓe.

A cewarsa, makomar Kano da Najeriya ta na hannun ‘yan ƙasa masu wayewa da kishin ƙasa, don haka ya kamata kowa ya yi rajista tare da shiga harkokin dimokuraɗiyya cikin lumana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!