Labarai
Gwamnatin Kano zata cigaba da yada da’awa
Gwamnatin Kano ta ce zata cigaba da yada da’awa a yankunan karkara da kauyuka, don daukaka kalamar Allah.
Daraktan hukamar shari’a na jihar Kano Malam Murtala Muhammad Adam ya bayyana cewa zasu cigaba da fadada aikin da’awa da suke musamman a cikin kauyuka da karkara domin kuwa da dama akan samu mutane da yawa da basu fahimci addini ba.
Gwamnatin Kano ta siyo kayayyakin yada Da’awa
Wannan bayani ne yayin da ake gabatar da wani taro da aka gabatar a kamar hukumar Rano da kibiya da Bunkure domin kara jawo hankalin masu yada da’awa da kuma kara musu karfin gwiwa.