Kiwon Lafiya
Gwamnatin kasar Jamhuriyar Nijar ta ce zata yi aiki da kasarnan don bunkasa ilimi
Gwamnatin kasar Jamhuriyar Nijar ta ce za ta rika aiki tare da takwararta ta kasar nan domin bunkasa ilimi tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Babban sakatare a ma’aikatar ilimi mai zurfi a Jamhuriyar ta Nijar Dr. Abarshi Magalma ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi wajen bikin yaye dalibai a jami’ar Maryam Abacha da ke Maradin Jamhuriyar Nijar.
Ya ce hadaka a bangaren ilimi zai matukar taimakawa wajen ci gaban kasashen biyu da ke makwabtaka da juna.
Da yake nasa jawabi daraktan kulla alaka na jami’ar ta Maryam Abacha da ke Maradi, Dr. Bala Muhammed Tukur, ya ce; jami’ar ta farfado da tsohuwar zumunci da ke tsakanin kasashen biyu wanda ya yi rauni tsawon shekaru sakamakon raba kan al’umma da turawa ‘yan mulkin mallaka su ka yi.
Wakilin mu Abdullahi Isah ya ruwaito cewa dalibai dari hudu da tamanin ne jami’ar ta ya ye a wannan shekara.