Labarai
Gwamnatin Najeriya za ta gina sabbin wuraren kiwo 94 a jihohi 10
Gwamnatin Najeriya za ta gina sabbin kebantattun wuraren kiwo guda 94 a jihohin kasar guda 10 don dakile rikicin da ke aukuwa tsakanin manoma da makiyaya.
Majalisar kula da tattalin arzikin kasa wadda mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta ne ta amince da hakan yayin taron da ta gudanar a jiya a Abuja.
A cewar Osinbajo samar da wuraren kiwon kebabbu wani bangare ne na taswirar shekaru goma domin bunkasa harkar kiwon dabbobi a kasar nan da gwamnati ta tsara.
Mataimakin shugaban kasar, ya kuma ce aikin zai lakume naira biliyan dari da saba’in da tara.
Farfesa Yemi Osinbajo ya kara da cewa, za a kashe naira biliyan saba’in cikin watanni goma sha daya masu zuwa don fara aikin.
Jihohin da za a gina wuraren kiwon sun hada da: Adamawa da Benue da Ebonyi da Edo da Kaduna da Nassarawa da Oyo da Filato da Taraba da kuma Zamfara.