Labarai
Gwamnatin Nijeriya ta Fadi lokacin kammala aikin hanyar dogo ta Kano zuwa Maraɗi
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce nan da ƙarshen shekarar 2025 zata kammala aikin hanyar dogo da ta tashi daga Kano zuwa Maraɗi da kuma buɗe jami’ar horar da harkar tafiye tafiye dake Daura a ƙarshen shekarar nan domin samin sauki a harkar sufuri a faɗin ƙasar.
Babban ministan sufuri Alhaji Sa’idu Ahmad Alƙali ne ya bayyana hakan a yayin da yake duba aikin haryar domin ganin yadda aikin yake gudana da yadda aka gina jami’ar horar da harkar tafiye tafiyen da kuma yadda za’a mayar da hankali wajen kammala su akan lokaci.
Ministan ya kuma ce ‘muhimmancin aikin yasa yanzu haka gwamnati zata mayar da hankali domin kammala shi da kuma buɗe jami’ar, tare da duba gyare-gyaren da ya kamata ayi kafin bude makarantar’
Da yake jawabi shugaban Jami’ar horar da harkar tafiye tafiye ta Muhammadu Buhari dake Daura Farfesa Umar Adamu Katsal yabawa ziyarar da yakai wannan Jami’ar duk da tarin ayyukan da ke gabanshi, Wanda hakan na nuni da cewa ya dau wannan makarantar da mahimmanci.
Freedom radio ta rawaito cewa ministan ya sami rakiyar manyan ma’aikata domin duba yadda aikin yake gudana.
Rahoton: Umar Abdullahi Sheka
You must be logged in to post a comment Login