Connect with us

Labarai

Gwamnatin Sokoto na shirin fara rabon kayan haihuwa kyauta

Published

on

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce za ta fara rabon kayan haihuwa kyauta ga mata masu haihuwa a asibitocin gwamnati, domin rage mace-macen mata da jarirai.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Abubakar, ne ya bayyana hakan a wajen taron gabatar da rahoton tantance ayyukan gaggawa na kula da mata masu nakuda da jarirai a jihar ta Sokoto.

Ya ce gwamnati za ta kuma samar da wutar lantarki mai amfani da hasken Rana a dakunan haihuwa, tare da inganta ayyukan kula da mata masu juna biyu.

Kwamishinan ya ce gwamnati na ƙoƙarin magance matsalolin jinkirin neman lafiya, jinkirin isa asibiti da kuma jinkirin samun ingantaccen magani, wanda ke haddasa mace-macen mata masu juna biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!