Labarai
Gwamnatin Taraba ta musanta rahoton da DMO ya fitar

Gwamnatin Jihar Taraba ta musanta rahotannin da ke yawa cewa bashin jihar ya kai naira tiriliyan Daya da biliyan dari biyu.
Kwamishiniyar Kuɗi ta jihar, Dakta Sarah Adi Enoch, ce ta ayyana hakan ga manema labarai.
Ta kuma ce, rahotannin ba suma yi daidai da adadin bashin da aka amince jiha ta ciyo a hukumance ba.
A wani taron manema labarai a Jalingo, ta ce bayanan Hukumar Kula da Basussukan Najeriya, DMO, sun nuna cewa bashin cikin gida na jihar ya kai naira biliyan 85 da digo 51, zuwa ƙarshen Disamban 2025.
Ta ce wannan adadi ya ragu da kusan naira biliyan 2 da digo 45, idan aka kwatanta da bashin kusan naira biliyan 87 da digo 96 da aka samu a baya.
You must be logged in to post a comment Login