Connect with us

Labarai

Za a kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano a Nuwamban bana- Dave Umahi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano nan da watan Nuwamba bana.

Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, ne ya bayyana hakan lokacin da shugabannin Kungiyar Dalibai na kasa, NANS, karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Babatunde Akinteye, suka kai masa ziyara a Abuja.

Sanata Umahi ya ce gwamnatin tarayya ta kashe sama da naira biliyan 200 wajen aikin, inda ya kara da cewa sama da kashi 80 cikin 100 na kudin aikin da ake gudanarwa a halin yanzu an biya.

Ministan ya kuma nuna damuwa kan yadda ake lalatawa tare da satar kayayyakin da ake amfani da su wajen gina manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.

Umahi ya ce gwamnatin tarayya za ta kara zuba jami’an tsaron da za su rika kula da babbar hanyar Abuja–Kaduna–Zariya–Kano, domin kare ta daga masu lalata kayayyakin aikin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!