Labarai
Ebola ta kashe mutane 2,011 a Kongo DR

Cutar Ebola ta kashe mutane 2,011 a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 4,381.
Hukumomin lafiya sun ce annobar, wadda aka sanar a hukumance a ranar 15 ga Mayun 2026, na yaduwa cikin sauri fiye da yadda aka taba gani a baya. Ana kuma zargin cewa cutar ta fara yaduwa tun watanni kafin a sanar da bullarta a hukumance.
Annobar ta shafi larduna biyar, kuma masana kiwon lafiya na fuskantar kalubale wajen dakile ta saboda rikice-rikicen tsaro, karancin kayayyakin kiwon lafiya da kuma wahalar gano mutanen da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar.
Wannan dai shi ne annobar Ebola mafi muni da Kongo ta fuskanta tun bayan wadda ta faru a shekarar 2018 zuwa 2020, kuma ta zama ta biyu mafi girma a tarihin duniya.
*Washington Post*
You must be logged in to post a comment Login