Labarai
Gwamnatin tarayya bata gudanar da ayyukan tituna yadda ya kamata ba
Ministar kudi, kasafin da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed, ta ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta yi isasshen aikin kan ayyukan titin ba.
Ta bayyana hakan ne jiya yayin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo.
Ministan ta ce kasar nan na da titinu da dama wandada basu cikin yanayi mai kyau, suke kuma bukatar gwamnatin tarayya ta shigo ciki domin gyara su.
Ta ce daga cikin manyan tituna da ke karkashin gwamnatin tarayya mafi yawansu basu da kyau, sannan akwai sauran tituna da ke karkashin kulawa gwamnatocin jihohi da su ma ke bukatar a gyara su.
Ta kara da cewar babban abin tambaya shine, shin gwamnati tayi aikin tituna yadda ya kamata ? sai ta ce bata yi, hakan ne ma ya sa akwai bukatar gudanar da ayyukan tituna da samar da wani shiri na musammam da za’a tara kudade domin gyara titunan kasar na.
Ministan ta ce a shekaru biyu da suka wuce gwamnati ta bada rancen da ta kira sukuku , a shekara ta 2017 don gina tituna 25, a shekarar ta 2018 kuwa aka gina tituna 23 sannan ake aikin wasu a yanzu haka.
Da take amsa tambayoyi dangane da batun da ministan ayyukan da gidaje Babatunde Fashola yayi na cewar ma’aikatarsa bata samu kudaden da ya kamata wajen gyara tituna, sai ta ce gwamnatin tarayya bata aiwatar da ayyukan kasafin kudi kaso dari bisa dari.
Ta ce ma’aikatar ayyuka da gidaje da ma’aikatar sufiri na daga cikin ma’aikataun da suke samun kulawar da ta dace daga gwamnatin tarayya a duk lokacin da aka fitar da kasafin kudi ko wasu kudade na yin mayan ayyuka.
Ta ce ma’aikatar ta na shirin fitar da naira biliyan 900 domin gudanar da ayyukan a watan disamban nan mai zuwa.
Ta ce tuni dai shugaba Buhari ya bada umarnin fitar da biliyan 650 domin gudanar da manyan ayyuka,a watan Oktoban da ya gabata a yayin da ya mika kasafin kudi na shekara ta 2020.