Labarai
Ana zargin Kare mai Cutar Hauka ya ciji Mutane 18 a Kano

Wani kare da ake zargin yana ɗauke da cutar hauka ya ciji mutane 18 a garin Garko da wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da shi a jihar Kano.
Rundunar Tsaron Dazuka ta Ƙasa, NFSS, ta ce karen ya ciji mutane 11 a Garko a ƙarshen makon da ya gabata, kafin ya wuce wasu al’ummomi ciki har da Raba, Kadage, Gurjiya da Dausai, inda ya ciji wasu mutane bakwai.
Kwamandan rundunar NFSS na jihar Kano, Abdullahi Al’ameen, ya ce an tura jami’an rundunar zuwa yankin domin bibiyar karnukan da ake zargin suna ɗauke da cutar.
Ya kuma buƙaci mutanen da karen ya ciza da su gaggauta zuwa asibiti domin samun kulawar lafiya.

You must be logged in to post a comment Login