Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata 25 ga Agusta 2026 a matsayin ranar hutun bikin Mauludi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga watan Agusta, 2026, a matsayin ranar hutun bikin Mauludi, don tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad ﷺ.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a yau Juma’a.

Ministan ya taya Musulmin kasar nan da sauran sassan duniya murnar wannan rana, tare da kira gare su da su yi tunani kan darussan tausayi, tawali’u da kuma hidima ga al’umma, wadanda suka kasance daga cikin kyawawan halayen rayuwar Annabi Muhammad ﷺ.

Ya ce wadannan dabi’u na daga cikin abubuwan da kasar nan ke matukar bukata a halin da take ciki, inda ya bukaci kowa da kowa, ba Musulmi kadai ba, da ya yi tunani a kansu.

Ministan ya kuma bukaci mutane da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da hadin kan kasa, yana mai cewa tabbatar da zaman lafiya da hadin kai nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!