Labarai
INEC ta sanya ranar zaɓen cike gurbi a kujeru biyu na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sanya ranar 19 ga Satumba ta 2026 domin gudanar da zaɓen cike gurbin a kujeru biyu na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi.
Zaɓen zai gudana ne a mazabar Sakwa da ke ƙaramar hukumar Zaki, da kuma Disina a ƙaramar hukumar Shira.
Kujerar Sakwa ta zama babu kowa A kai ne bayan rasuwar ɗan majalisar da ke wakiltar yankin, yayin da ɗan majalisar Disina ya yi murabus domin neman kujerar shugabancin ƙaramar hukuma.
Kwamishinan Zaɓe na INEC a jihar Bauchi, Umar Ibrahim, ya ce jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fidda gwani daga 21 zuwa 25 ga Agusta.
Ya ce kuma za a fara yakin neman zaɓe a hukumance daga 9 zuwa 17 ga Satumba, kafin gudanar da zaɓen a ranar 19 ga watan.
INEC ta bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su bi dokokin zaɓe da jadawalin hukumar, domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin gaskiya da lumana.
You must be logged in to post a comment Login