Labarai
Gwamnatin Tarayya ta bude iyakoki 6
Hukumar yaki da fasa kwauri ta Nijeriya Kwastam, ta ce gwamnatin tarayya ta sake bude wasu iyakokin kasar nan na tsandauri guda shida ammma bisa tsauraran matakan tsaro.
Mukaddashin shugaban hukumar Wale Adeniyi ne ya bayyana hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala ganawa da shugaba Bola Ahmad Tinubu.
Ya kara da cewa iyakokin kan tudu guda shida ne kawo yanzu gwamnati ta ba da umarnin sake budewa, amma za sanya ido sosai wajen hana safarar man fetur zuwa ketare, da ma sauran kayayyakin da aka haramta shigo da su.
Tun a cikin watan Agustan shekarar 2019 ne dai gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar nan na kan tudu, da nufin dakile ayyukan fasa kwauri da kuma bunkasa shirin samar da shinkafa ta cikin gida, ko da yake a watan Disambar shekarar 2020 gwamnatin ta sake ba da umarnin bude iyakoki hudu daga cikin su.
You must be logged in to post a comment Login