Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe kan iyakoki

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin Najeriya na sa’o’i 24 gabanin babban zaɓen  da ke tafe a ranar Asabar.

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar kula da shige da fice ta fitar a shafinta na Twitter wanda ya samu sa hannun shugabanta, Isah Jere Idris.

Sanarwar ta ce daga gobe Asabar za a rufe dukkanin iyakokin ƙasa har zuwa ranar Lahadi 26 ga watan Feburairu.

Idris Jere ya buƙaci dukkan shugabannin hukumar da ke kan iyakoki da su tabbata an bi wannan umarni, har ma ya ce, hukumar a shirye ta ke wajen ganin ta bayar da gudummawa na ganin an gudanar da zaɓukan lami lafiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!