Labarai
Gwamnatin tarayya ta musanta rahoton Bankin Duniya

Ma’aikatar Kuɗi ta Najeriya ta soki rahoton Bankin Duniya da ya nuna cewa kuɗin ruwa da gwamnatin tarayya ke biya kan basussukanta ya kai kashi 124 cikin ɗari na kuɗaɗen shiga a rabin farkon shekarar 2026.
Ma’aikatar ta ce rahoton ya haɗa da kuɗin ruwa kan basussukan ƙasashen waje da gwamnatin tarayya ke biya a madadin jihohi da sauran matakan gwamnati, amma aka kwatanta su da kuɗaɗen shigar gwamnatin tarayya kaɗai, lamarin da ta ce ya sa alkaluman suka zama masu ruɗarwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, ma’aikatar ta ce kuɗaɗen shigar gwamnatin tarayya sun ƙaru da kashi 72 cikin ɗari, daga naira tiriliyan 3.6 a rabin farkon shekarar 2025 zuwa tiriliyan 6.2 a shekarar 2026.
Ta ƙara da cewa kuɗin ruwa kan basussukan ya ƙaru da kashi 38 cikin ɗari, daga tiriliyan 5.6 zuwa tiriliyan 7.7, tana mai cewa hakan na nuna ci gaban da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnati suka samar.
You must be logged in to post a comment Login