Labarai
Gwamnatin Tinubu na fuskantar caccaka bayan fitar rahoton sabon rahoton IMF

Gwamnatin Najeriya na fuskantar sabon suka bayan cece-kuce da ya biyo bayan rahoton Asusun Lamuni na Duniya (IMF) cewa an kashe sama da naira tiriliyan 8 na kudaden gwamnati ba tare da bayyana su a bayanan kasafin kuɗi ba.
Rahotonni sun bayyana cewa, cece-kucen ya fara ne bayan rahotannin da suka danganta ga wakilin IMF a Najeriya, Christian Ebeke, wanda aka ce ya bayyana a wani taro da aka gudanar a Legas cewa an kashe kuɗaɗen gwamnati da suka kai kusan kashi biyu cikin ɗari na Jimillar Arzikin Ƙasa (GDP), amma ba a nuna su a bayanan kuɗaɗen gwamnati ba.
Bisa hasashen GDP na Najeriya na shekarar 2025 da ya kai kusan naira tiriliyan 441.5, adadin ya kai kusan naira tiriliyan 8.83.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin, yayin da ’yan adawa suka bayyana batun a matsayin abin damuwa matuƙa.
You must be logged in to post a comment Login