Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya zata baiwa manoman audiga fiye da 100 tallafi
Gwamnatin tarayya zata baiwa manoman Audiga fiye da dubu dari 100 tallafin bunkasa harkokin noman su karkashin shirin babban bankin nageriya a wannan shekarar ta 2019.
Karamar ministan ciniki da masanaantu Hajiya Aisha Abubakar ta bayyana haka a jiya laraba a Zariya ,yayin taron bitar yini guda da akayi domin samar da irin audiga da zai bunkasa noma a jihar Niger.
Taken taron bitar shine yadda za’a kara farfado da irin noman audiga mai inganci audiga domin bunkasa masanaatun kasar nan da suke sarrafa tufafi.
Karamin ministan ta samu wakilcin madam Omolulu Opeewe wadda darakta ce a ma’aikatar tace gwamnatin tarayya ta bawa tsarin noman audiga fifiko domin inganta noman sa a kasar nan.
Tace ci gaba da cewa, tsarin farfado da tatalin arziki yasa gwamnatin tarayya kokarin inganta noman audiga Najeriya
Ta kara da cewa,dalilin fito da shirin dan kara wa manoman cikin gida kwarin gwiwa dan bunkasa noman audiga .
Ministar ta kara da cewa,domin tabatta da tsarin shi yasa maaikatar tashigo da maaikatu da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki domin fito da sababbin hanyoyin zamani dan inganta noman audiga.