Labaran Wasanni
Gwamnatoci su samar da sahihan jagorori a bangaren wasanni- Faruk Yarma
Tsohon kwamishinan harkokin matasa da wasanni na jihar Gombe Alhaji Faruk Yarma, ya yi kira ga hukumomi a dukkanin matakai , da su samar da sahihan ingantattun jagororin wasanni wanda suke masana a harkar don bunkasa bangaren tun daga tushe.
Alhaji Faruk Yarma, ya yi wannan kiran ne a hira ta musamman da gidan Rediyon Freedom, wanda ya yi duba kan yadda harkokin wasanni a kasar nan yake samun koma baya.
Faruk Yarma, yace akwai takaici kwarai da gaske in har akayi duba da yadda harkokin wasanni yake in aka kwatanta shi da sauran takwarorin sa na kasashen duniya, musamman ta wajen ingantattun kayan wasanni, filaye da kuma su kansu jagororin dake gudanar da harkokin wasannin.Tsohon kwamishinan ya kara dacewa, da yawan masu rike da madafun iko a harkokin wasannin kasar nan, ba wanda suka san harkar bane ,basu kuma da kwarewa ko kaunar abin a zuciyar su, wanda hakan yasa ake samun matsalolin tafiyar da harkokin na wasanni ba yadda ya kamata ba.
Labarai masu alaka.
An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu
An fitar da sunayen wadan da za a karrama a bangren wasanni
Matukar muna son cigaba da kuma gyara a harkar, dole ne mu ragewa gwamnatoci nauyi na gudanar da al’amurran kungiyoyi tare da samar da kamfanunuwa masu zuba jari, ta yadda kungiyoyi zasu dogara da Kansu tare da samarwa da Kansu kudaden shiga inji tsohon kwamishinan.
Haka zalika, Faruk Yarma, ya yi suka bisa tsarin da ake dashi na lura da filayen wasanni da lafiyar ‘yan wasa, tare da alakanta sakaci da halin ko in kula wajen mutuwar dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Nassarawa United Chineme Martin’s , da ya Mutu a baya bayan nan.
Ya yi kira ga hukumar shirya gasar firimiya ta kasa (LMC) data dau matakin ba sa ni ba sabo, wajen daukar tsattsauran mataki akan dukkan kungiyar da ta karya dokoki kowanne iri ne da suka danganci wasa ko inganta
lafiyar ‘yan wasa, kasancewar ita ce hanyar da zata yi tasiri wajen saita kungiyoyin don bin ka’idoji da kiyayewa.
Harkoki na wasanni dole , sai kana tafiya da Zamani kuma sai kayi hakuri kasancewar tsari ne da yake tafiya a hankali ba mai bukatar gaggawa ba, don haka kalubale ne babba ga hukumomi su tanadar da wajen gudanar da wasannin , wanda hakan zai janyo masu saka hannun jari a cikin harkar, da zata amfani matasa da samar musu sana’o’in yi da dogaro da Kansu, a gefe daya ta samarwa da gwamnatocin makudan kudade inji tsohon shugaban gudanar da kungiyar Kwallon kafa ta Gombe United , wanda kuma shi ne ma mallakin kungiyar Yarmalight Fc, dake jihar ta Gombe.
You must be logged in to post a comment Login