Connect with us

Labaran Wasanni

 Gwamnatoci su samar da sahihan jagorori a bangaren wasanni- Faruk Yarma

Published

on

Tsohon kwamishinan harkokin matasa  da wasanni na jihar Gombe  Alhaji Faruk Yarma, ya yi kira ga hukumomi a dukkanin matakai , da su samar da sahihan ingantattun jagororin wasanni wanda suke masana a harkar don bunkasa bangaren tun daga tushe.

Alhaji Faruk Yarma, ya yi wannan kiran ne a hira ta musamman da gidan Rediyon Freedom, wanda ya yi duba kan yadda harkokin wasanni a kasar nan yake samun koma baya.

Faruk Yarma, yace akwai takaici kwarai da gaske in har akayi duba da yadda harkokin wasanni yake in aka kwatanta shi da sauran takwarorin sa na kasashen duniya, musamman ta wajen ingantattun kayan wasanni, filaye da kuma su kansu jagororin dake gudanar da harkokin wasannin.Tsohon kwamishinan ya kara dacewa, da yawan masu rike da madafun iko a harkokin wasannin kasar nan, ba wanda suka san harkar bane ,basu kuma da kwarewa ko kaunar abin a zuciyar su, wanda hakan yasa ake samun matsalolin tafiyar da harkokin na wasanni ba yadda ya kamata ba.

Labarai masu alaka.

An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu

An fitar da sunayen wadan da za a karrama a bangren wasanni

Matukar muna son cigaba da kuma gyara a harkar, dole ne mu ragewa gwamnatoci nauyi na gudanar da al’amurran kungiyoyi tare da samar da kamfanunuwa masu zuba jari, ta yadda kungiyoyi zasu dogara da Kansu tare da samarwa da Kansu kudaden shiga inji tsohon kwamishinan.

Haka zalika, Faruk Yarma, ya yi suka bisa tsarin da ake dashi na lura da filayen wasanni da lafiyar ‘yan wasa, tare da alakanta sakaci da halin ko in kula wajen mutuwar dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Nassarawa United Chineme Martin’s , da ya Mutu a baya bayan nan.

Ya yi kira ga hukumar shirya gasar firimiya ta kasa (LMC) data dau matakin ba sa ni ba sabo, wajen daukar tsattsauran  mataki akan dukkan kungiyar da ta karya dokoki kowanne iri ne da suka danganci wasa ko inganta

lafiyar ‘yan wasa, kasancewar ita ce hanyar da zata yi tasiri wajen saita kungiyoyin don bin ka’idoji da kiyayewa.

Harkoki na wasanni dole , sai kana tafiya da Zamani kuma sai kayi hakuri kasancewar tsari ne da yake tafiya a hankali ba mai bukatar gaggawa ba, don haka kalubale ne babba ga hukumomi su  tanadar da  wajen gudanar da wasannin , wanda hakan zai janyo masu saka hannun jari a cikin harkar, da zata amfani matasa da samar musu sana’o’in yi da dogaro da Kansu, a gefe daya ta samarwa da gwamnatocin makudan kudade inji tsohon shugaban gudanar da kungiyar Kwallon kafa ta Gombe United , wanda kuma shi ne ma mallakin kungiyar Yarmalight Fc, dake jihar ta Gombe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Coronavirus

Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da shigar Cutar Coronavirus cikin ma’aikatan lafiya a wasu asibitoci biyu dake jihar.

Kwaminshinan lafiya na jihar kuma shugaban kwamaaitin dakile yaduwar cutar ta Covid-19 a jihar, Dr. Abba Umar ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Dr. Abba ya ce asibitocin da abin ya faru sun hada asibitin Rashid Shakoni dake Dutse sai kuma asibitin gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu (FMC-BKD).

Dr. Abba ya kara da cewa na Rashid Shakoni din sun dauki cutarne a wurin wata mai juna biyu da aka kawota daga karamar hukumar Miga wadda bayan ‘yan kwanaki ana bata kulawa, alamu suka nuna tana dauke da cutar Covid-19 kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi mata ya nuna wadda itace mutum na biyu da ta rasu sanadiyyar cutar a Jigawa.

Karin Labarai:

Ma’aikatan jinya 18 sun kamu da Corona a Kano

Ma’aikatan lafiya 14 sun kamu da Corona a Katsina

Ma’aikatan lafiya 7 sun kamu da Coronavirus a Borno

Haka abin yake a asibitin Tarayya na Binin Kudu can ma dai wani marar lafiyane ya kwanta, wadda daga karshe shima aka gwadashi ya kamu da cutar.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito kwaminshinan na cewa tuni dukkan likitoci da jami’an lafiyar da suka kula da wadancan mutane an killacesu kuma harma an gano wasu daga ciki sun kamu da cutar, duk da har kawo yanzu yace basu gama kididdige ko jami’an lafiya nawa ne cutar ta shafa fa.

Wannan dai na zuwa ne yayinda ake ta samun rahotonnin jami’an lafiya dake kamuwa da cutar ta Covid-19 a sassa daban-daban na kasarnan.

A makociyar jihar Jigawan wato Kano kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar ta tabbatarwa da Freedom Radio cewa Likitoci 34 ne suka kamu da cutar a jihar zuwa makon da muke ciki.

Haka abin yake inda suma ma’aikatan jinya da unguzoma 18 suka kamu da cutar a jihar Kanon.

Ita ma jihar Katsina dake makotaka da jihar Jigawan gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa wasu jami’an lafiya a jihar sun kamu da cutar ta Covid-19.

Continue Reading

Labaran Kano

Kano Pillars ta jajantawa dan wasanta Rahakku .

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta mika sakon ta’aziyyar ta ga dan wasanta Rahakku Adamu, wanda dan sa Muhammad Rahakku, ya  rasu a ranar talatar data gabata.

A  wata sanarwa da kakakin kungiyar Rilawanu Idris Malikawa Garu, ya sakawa hannu kuma aka saka a shafin Twitter na kungiyar, sanarwar ta nuna alhinin dukkanin ‘yan tawagar kungiyar tare da mika ta’aziyyar su ga iyalin dan wasan.

Labarai masu alaka.

Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana

Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu

Haka zalika sanarawar tayi addu’ar samun rahama da dacewa ga marigayin.

Continue Reading

Labaran Wasanni

Covid- 19: Zamu dawo gasar Serie A Gabrielle Gravina

Published

on

 

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Italiya, (FIGC)Gabriele Gravina, yace zasu dawo karasa gasar kakar wasan bana na shekarar 2019/20.

An dai dakatar da gasar ta kasar Italiya,  a watan jiya, sakamakon bullar cutar Corona, wanda hukumar tace ba za’a dawo gasar ba har sai an tabbatar da kawar da cutar.

Gwamnatin kasar Italiya a baya, ta kara wa’adin killace al’umma da zirga zirga, zuwa ranar 03 ga watan Mayu, sai dai rahotanni daga kasar ta Italiya, sun tabbatar dacewar kungiyoyin gasar sun bukaci dawowa a cikin wannan watan don kammala gasar kakar bana, a cikin watan Yuli.

Wasu kungiyoyin basa goyon bayan dawowa cigaba da gasar, sai dai kuma Gravina yace akwai yunkurin dawo wa akan lokaci do cigaba da gudanar da gasar.

Labarai masu alaka.

Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni

An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona

Fatan mu shi ne fara gasar da wuri,inji Gravina  don kammala ta kan lokaci  kasancewar rashin yin hakan  zai kawo koma baya kwarai da gaske

Zuwa yanzu haka cutar ta Coronavirus ta kashe mutum 114,170 a fadin duniya cikin mutum 1,851,400 da suka kamu da cutar.

Daga kasar ta Italiya an samu mutuwar mutum  19,890 a cikin mutane 156,360  da suka kamu da cutar.

 

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,396 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!