Labarai
Gwamnonin Arewa sun kafa Asusun Tsaro tare da rantsar da kwamitin amintattu

Gwamnonin jihohin Arewa sun kafa Asusun Tsaron Arewacin Najeriya, tare da rantsar da kwamitin amintattu da zai kula da tafiyar da asusun.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro wajen yaƙi da matsalolin ‘yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.
Ya ce asusun zai taimaka wajen tattara kuɗaɗe, inganta musayar bayanan sirri da kuma tallafa wa ƙoƙarin hukumomin tsaro na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma ya jaddada cewa dole ne a magance tushen matsalolin rashin tsaro da suka haɗa da talauci, jahilci, rashin aikin yi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
You must be logged in to post a comment Login