Labarai
Gwmanatin tarraya ta fito da sabon tsarin tallafawa ‘yan Nigeriya
Majalisar kula da Tattalin Arziƙi ta Nigeriya ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta ɗauka don samar wa ‘yan ƙasa sauƙin rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.
Majalisar ta sanar da matakan ne a ƙarshen taron wata-wata da ta yi ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jingine batun raba kuɗin tallafi na naira 8,000 ga gidajen talakawa miliyan 12 a faɗin ƙasar na tsawon wata shida.
Jingine batun tallafin na naira 8,000 ya biyo bayan sukar shirin da al’umma suka yi, bayan amincewa da yin hakan da shugaban ya samu daga Majalisar Dokoki ta ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login