Connect with us

Labarai

Zan rage farashin Fetur da gas da man jirgi zuwa naira 200 duk lita dan takarar- SDP

Published

on

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ce zai rage farashin man fetur, gas ɗin girki da man jiragen sama zuwa naira 200 kan kowace lita, cikin watanni 12 bayan kama mulki idan aka zaɓe shi a 2027.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da maneman labarai a Abuja in da ya ce zai farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma ƙarfafa aikin matatun mai ƙanana, domin rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

 

Adebayo ya kuma yi alkawarin rage kuɗin sufuri da gidaje, tare da samar da ilimi da kiwon lafiya kyauta, da kuma bai wa noma da samar da abinci muhimmanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!