Labarai
Hakkin miji ne ya bai wa matarsa cikakkiyar tarbiyya bayan aure – Farfesa
Kwamitin bibiyar al’amuran da suka shafi auratayya ta Jihar Kano ya ce hakkin miji ne ya bai wa matarsa cikakkiyar tarbiyya bayan aure.
Sakataren kwamitin Farfesa Usman Zunnuraini ne ya bayyana hakan a yau ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom, wanda ya maida hankali kan hanyoyin da za a bi don rage yawaitar mace-macen aure.
Ferfesa Usman Zunnurainin ya kara da cewa, kamata ya yi kowacce mace tasan hakkin mijinta kuma shi ma miji yasan hakkinsa, da nufin kawo zaman lafiya a tsakaninsu.
Yana mai cewa, rashin tsafta da rashin adana dukiyar miji na kawo raguwar soyayya tsakanin ma’aurata, a cewa sa, babu wani dalili da zai sa miji ya boye wa matarsa karin auren saboda wani dalili na kashin kansa.
Farfesa Zunnuraini ya kuma yi kira ga ma’aurata da su kasance masu biyayya da aure kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
You must be logged in to post a comment Login