Labarai
Har yanzu ba a saki sakamakon jarrabawar NECO na ɗaliban Kano ba
Ɗaliban jihar Kano da suka rubuta jarrabawar kammala sakandire ta NECO sun koka kan rashin sakin jarrabawarsu.
Rahotonni sun ce, hakan ya biyo bayan rashin biyan kuɗin jarrabawar ɗaliban daga Gwamnatin Kano.
Tun a ranar Laraba 13 ga watan Janairun da muke ciki ne hukumar shirya jarrabawar ta NECO ta sanar da sakin sakamako ga ɗalibai.
Sai dai ɗaliban makarantun Gwamnatin Kano sun gaza samun nasu sakamakon idan sun duba.
Karin labarai:
Kano: Yawan ƙuri’un zaɓen ƙananan hukumomi sun zarce na zaɓen Gwamnan 2019
An bankaɗo maɓoyar masu garkuwa da mutane a Kano
Wasu ɗalibai sun shaida wa Freedom Radio cewa, cikin kwanaki biyar sanarwar sakin jarrabawar sun sayi katin kankara amma suna gwadawa ba sa ganin sakamako.
Tun a watan Agusta na shekarar 2020 ne dai, Gwamnatin Kano ta ce, ta ware kuɗi har miliyan 489 domin biyan kuɗin jarrabawar ɗaliban.
Inda ta ce, za biya wa ɗaliban da suka samu aƙalla Kiredit biyar waɗanda suka haɗa da darasin Lissafi da ba Turanci.
Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Kwamishinan Ilimi na Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Ƙiru kan wannan batu, amma har kawo lokacin haɗa wannan rahoto bamu samu ji daga gare shi ba.
You must be logged in to post a comment Login