Kasuwanci
Har yanzu bamu farfado daga mashash-sharar Corona ba – Masu kananan sana’o’i
Masu kanana da matsakaitan sana’oi a Kano na ci gaba da kokawa sakamakon koma baya da suka ce sun samu sanadiyyar cutar corona.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin Kano ta dage dokar kulle da ta sanya don dakile yaduwar cutar covid-19, lamarin da ya sanya al’amuran yau da kullum su ka fara dawowa kamar yadda suke a baya.
Sai dai ga bangaren masu rini har yanzu ba ta sauya zane ba, domin kuwa a cewar su, tsawon watanni da aka yi a gida, ya janyo musu asara mai yawa.
Alhaji Audu Yahaya dattijo ne da ya kwashe sama da shekaru saba’in yana gudanar da sana’ar rini a marina ta Kofar Mata da ke nan birnin Kano, a yayin zantawarsa da wakilin freedom rediyo Abdullahi Isah, ta cikin shirin Idon Freedom, ya ce, su kam har yanzu tsugune ba ta kare ba.
Malam Yakubu Bashir wani magidanci ne da ke gudanar da sana’ar gyaran babur a unguwar Fagge, a zantawarsa da Shamsu Da’u Abdullahi, ya ce, garesu lamura basu koma kamar yadda suke a baya ba.
Malam Saleh Audu wani dattijo ne da ke gudanar da sana’ar suyar kifi a unguwar Dan Maliki da ke yankin karamar hukumar Kumbotso, ya ce, rashin jari ne babbar matsalarsa a yanzu, domin kuwa tuni ya cinye jarinsa a zaman gida da aka yi na sama da watanni biyu.
Malam Saleh Audu ya kuma yi kira ga hukumomin da kuma masu hannu da shuni da su taimaka musu don farfadowa da halin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.
You must be logged in to post a comment Login