Coronavirus
Hisba ta bukaci al’umma subi dokar hanafita da gwamnatin Kano ta sanya
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya ja hankalin al’umma wajen yin hakuri tare da yin biyayya ga umarnin da gwamnatin jiha ta dauka na hana zirga-zirga, wanda ya ce an yi hakan ne don kiyaye lafiyar al’umma.
Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da Wakilin mu Umar Idris Shu’aibu ta kafar sada zumunta ta WhatsApp.
Ya ce ya zama wajibi mutane suyi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’in neman saukin rayuwa da kare al’ummar musulmi daga dukkan annobar dake tunkarowa.
Ta cikin tattaunawar babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina ya ce bin shawarwarin likitoci da suke bayarwa, musamman na rage cunkoso da wanke hannaye zai taimaka gaya wajen kare dimbin al’umma.
Ustaz Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya Kara da cewa, musulmi sun san da cewar, irin wannan matakai ba sabbi bane a addinin musulunci, ta fuskar daukar mataki kan kowacce matsala tun ma kafin ta auku.
Matakin hana shigowa wani gari ko kuma hana fita ya samo asali ne daga tsari irin na addinin musulunci, don hana yaduwar cutuka ko kuma wata barna da ka zata iya yin illa ga rayuwar mutane.
Ibn Sina sai dai ya ja hankalin Gwamnati da hukumomi da nauyin al’umma ya rataya a wuyan su kai tsaye, da kuma mawadata da Allah (S.W.T) yayiwa arziki da su himmatu wajen tallafawa mutanen da ke kusa da su da abinci da sauran kayan masarufi na yau da kullum, don samun saukin rayuwa, wanda matakin ka iya sanya mahalicci ya saukar da ni’imomin sa a cikin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login