Labarai
Hisba ta sha alwashin cafke matasan da ke aikata laifuka a Masallatai

Hukumar Hisba ta ce za ta hukunta duk wanda ta samu ya na aikata ba dai-dai ba a masallatan da ake gudanar da sallar Ittikafi musamman ga samari da yan Mata.
Mataimakin Babban kwamandan Hisbah na Kano Dakta Mujahiddin Aminuddin ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya raba ga manema labarai.
Ya kuma ce hukumar ta baza jami’an ta masallatai dan sanya idanu a wannan lokaci da aka shiga goman karshe na watan Azumin Ramadana.
You must be logged in to post a comment Login