Labaran Kano
Hisbah bata da hurumin yin bulala ko cin tara ga mai laifi -Barista Sunusi Musa
Wani lauya a nan Kano Barista Sanusi Musa ya bayyana cewa ko kadan hukumar Hisbah bata da hurumin yin bulala ko cin tara ga wanda ta kama da aikata wani laifi.
Yayin wata zantawa da lauyan yayi da Freedom Radio kan yunkurin hukumar Hisbah ta jihar Kano na fara cafke masu cakuda maza da mata a baburan adai-daita sahu daga farkon shekara mai kamawa kamar yadda babban kwamandan hukumar Hisbahn Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina ya bayyana.
“Duk abinda ma’aikatan Hisbah da Kwamandanta zasuyi dole ya zama iya abinda dokar hukumar ta tanadar musu, sannan koda dokar Hisbah ta tanadar da cewa idan mutum ya cakuda maza za’ayi masa bulala, to a kundin tsarin mulkin Najeriya hukumar Hisbah bata da hurumi na aiwatar da wannan dokar, Kotu ce kadai take da hurumin aiwatarwa, aikin Hisbah shi ne in sun kama mutum su kaishi gaban alkali, kuma a tabbatar an bashi dama ya kare kansa, Kotu ce zata yanke cewa ayi masa bulala ko ayi masa tara” a cewar Barista Sunusi Musa.
Kazalika Barista Sunusi Musa ya kara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya raba tsarin gida uku akwai bangaren masu yin doka sune ‘yan majalisa sannan akwai bangaren masu zartarwa nan ne inda Hisbah ta ke, sannan akwai kuma bangaren Shari’a wanda nan ne inda ake tabbatarwa mutum yayi ko baiyi ba.
A karshe Barista Sunusi Musa ya shawarci hukumar Hisbah kan duk lokacin da irin wannan ta taso akwai bukatar su nemi gudummuwar bangaren lauyoyi masana shari’a don gudun kar garin neman gira a rasa idanu.