Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hisbah za ta tura dakarunta masallatan da ake gudanar da Tuhajjudi

Published

on

Hukamar Hisbah ta jihar Kano, ta sanar da shirin tura Dakarun kar ta kwana, a wuraren da jama’a ke gudanar da sallar dare, domin samar da tsaro da sa ido don magance dabi’ar kwacen waya da matasa masu yin zance da yan mata, kan yi a lokutun sallar dare.

Babban kwamanda hukumar Hisbah, Dakta. Harun Ibin Sina shine ya baiyana hakan a shalkwatan hukumar da ke unguwar Sharada.

Dakta Harun Ibin Sina ya ce ‘zasu tura dakarun nasu ne domin tabbatar da anayin abinda ya kamata, tare da tsare dokiyoyin al’umma, musamman ma ababen hawan da suka je gudanar da ibadar’.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!