Labarai
Hukumar Civil Defence ta cafke matasa fiye da 70 dauke da makamai
Hukumar tsaro ta Civil Defence shiyyar Kano ta ce, ta kama matasa su fiye da 70 da tarin makamai da ake zargin su da tayar da hankalin al’umma da fashe fashen motoci harma da ƙona su.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar DSC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana hakan da yammacin yau Alhamis yayin taron manema labarai da hukumar ta gudanar a shalkwatar hukumar da ke kan titin zuwa Zaria.
Ya ƙara da cewa za su ci gaba da baza jami’ai domin kama duk wasu masu tada zaune tsaye.
You must be logged in to post a comment Login