Kiwon Lafiya
Hukumar ICRC zata shiga tsakanin don sasanta hukumar filayen jiragen sama da wani kamfani
Hukumar kula da jinginar da kadarorin gwamnati ta kasa ICRC ta ce za ta shiga tsakani domin sasanta hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa da wani kamfani mai zaman kansa da ke kula da sashen karbar baki masu dawowa da tantance masu fita na biyu a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos mai suna Bi-Courtney Aviation Services Limited.
Shugaban hukumar ta ICRC Chidi Izuwah ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai filin jirgin saman na Murtala Muhammed da ke Lagos.
Ya ce tuni hukumar ta tuntubi karamin Ministan zirga-zirgar jiragen sama Hadi Sirika domin samo mafita kan matsalar.
A shekarar 2003 ne dai gwamnatin tarayya ta jinginar da sashen karbar baki masu dawowa da tantance masu fita na biyu na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos ga wani kamfani mai suna BASL, sai dai daga bisani an samu matsaloli da dama wadanda suka dabai-baye batun jinginar da sashen.