Labarai
Hukumar INEC ta kara wa’adin karbar katin zabe
- INEC ta karin wa’adin mako guda
- Karin wa’adin zai bada dama ga wadanda ba su karbi nasu ba
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta sanar da yin karin wa’adin mako guda a bisa ranakun da za a kammala karbar katin yin zaben a cibiyoyin hukumar a fadin Najeriya.
Mai magana da yawun hukumar INEC a Kano Adam Ahmad Maulud, ne ya sanar da hakan a zantawarsa da Freedom Radio a safiyar yau.
Adam Ahmad Maulud ya ce, karin wa’adin zai bada dama ga wadanda ba su karbi na su ba, su je su karba kafin cikar wa’adin.
Rahoton: Hafsat Abdullahi Danladi
You must be logged in to post a comment Login