Connect with us

Labarai

Hukumar REMASAB a Kano ta kama jabun lemuka

Published

on

Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano REMASAB ta ƙwato wasu lemon roba da wa’adin amfani da su ya ƙare a Kasuwar Malam Kato da ke Kano.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Malam Abubakar Ahmad ya fitar a ranar Jumuʼa 17 ga Afrilu 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa, an gano kayayyakin ne yayin wani samame da kwamitin “Karta-Kwana” na hukumar ya gudanar bisa umarnin Shugaban Hukumar, Dr. Muhammad S. Khalil.

A cewar sanarwar, an tarar da wani shago dauke da lemon robar da wa’adinsu ya ƙare, inda nan take aka kwace su tare da mika su ga hukumar kare hakkin masu saye domin daukar matakin da ya dace.

A ci gaba da rangadin, kwamitin karkashin jagorancin Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga na hukumar Malam Aliyu Tukur, ya kai ziyara a titin BUK daura da Kofar Famfo, inda aka samu masu sana’o’i suna gudanar da harkokinsu cikin rashin tsafta.

Nan take aka tilasta musu tsaftace wuraren tare da kawar da sharar da suka zubar, yayin da aka kuma bai wa wasu shaguna takardun gargadi sakamakon karya dokokin tsafta.

Haka kuma, kwamitin ya kai ziyara titin Sheikh Ja’afar da ke Dorayi, inda aka samu wasu ’yan kasuwa na gudanar da sana’o’insu a gefen titi cikin rashin tsafta, inda aka umarce su da su gyara wuraren nan take.

A titin Katsina kuwa, kwamitin ya tabbatar da cewa wuraren da aka taba gyarawa na ci gaba da kasancewa cikin tsafta, abin da ke nuna tasirin ayyukan sa ido da wayar da kai.

Shugaban Hukumar, Dr. Muhammad S. Khalil, ya bukaci masu sana’o’i su rika tsaftace wuraren kasuwancinsu akai-akai, musamman masu sana’a a gefen hanyoyi, domin kare muhalli da kuma bunkasa kasuwancinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!