Kiwon Lafiya
Hukumar kula da fansho ta kasa ta ce jihohi 12 ne kacal su ke ba da kasonsu na tsarin fansho
Hukumar kula da fansho ta kasa (PENCOM), ta ce jihohi goma sha biyu ne kacal cikin jihohin da suka gabatar da dokar fansho suke ba da kasonsu cikin tsarin fanshon karo-karo ga ma’aikatansu a alkaluman da suka tattara a karshen watan Yunin shekarar da ta wuce.
Hakan na cikin kundin rahoton fanshon ma’aikatan jihohi da hukumar kula da fansho ta kasa ta fitar.
A cikin rahoton dai hukumar ta PENCOM ta ce jihohi goma sha biyu sun ba da hadin kai wajen bada kasonsu.
Hukumar ta PENCOM ta kuma ce jihohi 27 sun aiwatar da dokar fansho ta kasa yayin da dokar ke matakin kudiri gaban majalisun dokokin wasu jihohi guda takwas.
A cewar hukumar ta PENCOM, jihohin da ke ba da kasonsu cikin tsarin fanshon na kasa sun hada da: Lagos da Ogun da Kaduna da Niger da Delta da Osun da kuma Rivers.