Manyan Labarai
Hukumar NAFDAC ta dakatar da kamfanin pure water 17 a jihar Kaduna
Hukumar da ke kula da magunguna da ingancin abinci wato NAFDAC ta tsayar da wasu kamfanonin sarrafa ruwan leda goma sha bakwai aiki a jihar Kaduna sakamakon wasu laifuka da suka aikata.
Shugaban hukumar Mr Natim Mullah-Dadi ne ya bayyana haka a lokacin da suka kai ziyarar gani da ido wadannan kamfaninka a yunkurinsu na tabatar da an bi doka an sarrafa wannan ruwa cikin tsafta da tsari.
Ya bayyana cewa wadannan kamfanoni na gudanar da ayyukansu ne ba bisa ka’ida ba, wasu daga cikinsu kuma suka canza wuraren da suke sarrfa ruwan ba tare da izinin hukumar NAFDAC ba, yayin da wasu lasisi da wa’adin da ake ajeye wa ruwan ya wuce.
Ya kara da cewa duk kamfanin da suka rufe sakamakon makamancin wannan laifi ne, kuma ana dakatar da su ne har sai sun bi doka.
Mullah-Dadi ya ce hukumar ta shiga cikin damuwa sakamakon rashin kyauwun indan ake sarrafa wannnan ruwa , inda ya ce sun kwace wasu kayan aiki da injinan da suke amfani da su a kamfanin har sai kun bi ka’idojin da aka gindaya musu.
Ya kuma ja hankalin masu harkar pure water da su kauracewa amfani da wuri mara tsafta sannan su tabbatar suna gudanar da aikinsu ne bisa ka’idoji da izinin da aka basu.
Sun kuma ja hankalin jama’a da su tabbata sun lura da lamba NAFDAC kafin su sayi ruwan da zasu sha