Labarai
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi a Kano
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun samu nasarar kwace kwayoyin Tramadol da nauyinsu ya kai kilogram uku da rabi a filin Jirgin saman Malam Aminu Kano.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Jonah Achema ya fitar, ta ce kwayoyin mallakin wani ne mai suna Usman Hassan Ramadan mai shekaru 51, wanda shi ma ya shiga hannu.
LABARAI MASU ALAKA
NDLEA ta kama masu fataucin miyagun kwayoyi a Kano
Hukumar NDLEA ta kama mutane 2 bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi
Hukumar NDLEA: Sun koka na yadda matasa ke ta’amali da kwayoyin Tramadol
Jonah Achema ya bayyana cewa Usman Ramadan ya yi ikirarin cewa shi tsohon soja ne kuma ya fito ne daga Jihar Borno, inda suka kama shi a wajen binciken mutane a daidai lokacin da yake shirin hawa Jirgin Ethiopian Airline don zuwa birnin Dubai na hadaddiyar Daular Larabawa.
Mr Achema ya kara da cewa sun gano kwayar ne a cikin jakar wanda ake zargi inda ya bayyana musu cewa garin doya ne, said dai bayan an gano kwaya ce sai ya amsa cewa hakika kwayar Tramadol ce ya mayar da ita gari.
You must be logged in to post a comment Login