Labarai
Za a samu saukin kudin sufuri daga ranar 1 ga Oktoba- Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce, daga ranar 1 ga watan Oktoba mai kama wa za a samu saukin kudin sufuri a fadin Najeriya.
A wannan lokaci dai gwamnatocin jihohin kasar nan sun fara daukar matakai daban-daban wajen aiwatar da shirin amfani da iskar gas ta CNG.
Shirin ya biyo bayan taron da Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi kasar nan 36 suka gudanar a ranar 27 ga Agusta.
Fadar Shugaban Kasa ta ce, sama da motoci dubu 120 sun riga sun sauya zuwa amfani da makamashin CNG, yayin da ake da cibiyoyin sauya motocin sama da guda 400 da kuma wuraren sayar CNG sama da guda 90 a fadin kasaNajeriya.
You must be logged in to post a comment Login