Labarai
Hukumar NIMS za ta yiwa daliban makarantun furamare dana sakandare katin dan kasa kyauta

Hukumar yin katin dan kasa NIMS ta ce za ta yiwa daliban makarantun Furamare dana sakandare katin Dankasa kyauta.
Hakan na cikin wata ziyara da jami’in hukumar mai kula da shiyyar Kano Emmanuela Igbinovia ya kaiwa ma’aikatar Ilimi.
Ya kuma ce hakan na da nasaba da yadda ake bukatar katin dan kasa na NIN ga daliban da za su rubuta jarrabawar WAEC da NECO.
Da yake karin haske shugaban hukumar a nan Kano Garba Balarabe cewa ya yi duba da rashin mutanan da sukayi katin a nan Kano ne yasa suka fito da tsarin.
Kwamishinan Ilimi na Kano Ali Haruna Makoda da babban sakatare a ma’aikatar Malam Bashir Baffa ya wakilta cewa ya ce wannan ci gaba ne me kyau.
You must be logged in to post a comment Login