Labarai
An kama ‘yan China da ‘yan Najeriya 9 a wurin haƙar ma’adanai a Nasarawa

Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya, NSCDC, ta gurfanar da wasu ‘yan kasar China 15 da kuma ‘yan Najeriya tara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin gudanar da haƙar ma’adinan lithium ba tare da izini ba a jihar Nasarawa.
Rahotanni sun ce an kama mutanen ne a ranar 16 ga watan Mayun 2026 a ƙaramar hukumar Kokona, inda ake zarginsu da gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai a wani yanki da ke ƙarƙashin lasisin binciken ma’adinai mallakin kamfanin TIMADIX Geomin Consult Limited.
Alƙaliyar kotun, Mai Shari’a Ofili-Ajumogobia, ta amince da bayar da belinsu bayan lauyansu ya tabbatar da cewa za su ci gaba da halartar zaman kotu. Kotun ta umurce su da miƙa fasfofinsu da katunan shaidar zama ɗan ƙasa ga ma’ajin kotu.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Yuni domin ci gaba da shari’a. Hukumar NSCDC ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin dakile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare albarkatun ƙasar Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login