Labarai
Hukumar PCACC ta kama mutane biyu da ke sayar da takardun daukar aiki na bogi

Hukumar Karɓar Korafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta kama wasu mutane biyu, Abdul’aziz Muhammad Wudil da Isyaku Sale, bisa zargin su da siyar da takardun ɗaukar aiki a hukumar kula da manyan makarantun Sakandare KSSMB na bogi.
Da ya ke jawabi ga manema labarai, shugaban hukumar Kwamared Sa’idu Yahaya, ya ce, binciken hukumar ya nuna cewa wadanda aka kamadin sun karɓi kuɗin wasu mutane goma, har kimanin naira dubu dari uku daga kowannensu, sai dai daga bisani aka gano cewa, takardun daukar aikin na boge ne tare da gano irin su har guda 36 a gidajensu.
Shugaban hukumar ta Karɓar Korafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawar, ya kara da cewa, za su gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
Abdul’aziz Muhammad Wudil da kuma Isyaku Sale sun bayyana yadda su ke samun masu neman aiki tare da sayar musu da takardun, inda suka amsa cewa gaskiya ne sun sayar musu da takardun daukar aikin na bogi.
A ɓangaren masu ƙorafi kuwa, sun ce sun tura kuɗaɗen ne cikin zaton za su samu aiki na gaskiya, inda su ka sayar mu su da duk takarda guda a kan naira 300,000, bisa sharadin biyan naira 150,000 tare da cewa za su cika kimanin 150,000 bayan fara aikin.
You must be logged in to post a comment Login