Connect with us

Labarai

Farashin ɗanyen man Brent ya yi tashin goron zabi a kasuwar duniya

Published

on

Farashin ɗanyen man Brent ya haura dala 100 kan kowace ganga a kasuwar duniya a yau Laraba.

 

Rahotonni sun bayyana cewa, wannan ne karon farko tun watan Yuli da farashin mai ya haura dala 100, yayin da ake ci ga gaba da zaman ɗar-ɗar a Gabas ta Tsakiya.

 

Farashin man ya ci gaba da hauhawa a hankali a cikin ƴan makonnin nan, har ya haura dala 100.

 

BBC ta ruwaito cewa, harin da ƴan Houthi na Yemen suka kai kan cibiyoyin mai na Saudiyya a wannan makon ya haddasa gobara a cibiyar.

 

Haka kuma ta kara da cewa, lamarin na iya yin barazana ga jigilar ɗanyen mai ta Tekun Maliya, wadda ke zama wata hanya ta daban bayan mashigar Hormuz.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!