Labarai
Kungiyar Kamfanonin Jiragen sama ta yi barazanar dakatar da jigilar fasinjoji

Kungiyar Kamfanonin sufurin Jiragen saman kasar nan ta yi gargadin cewa kamfanonin jiragen sama a fadin kasar za su iya dakatar da ayyukansu daga ranar 20 ga Afrilun da muke ciki. Sakamakon hauhawar farashi mai.
A cikin wata wasika mai kwanan wata 14 ga Afrilu, 2026, mai dauke da sa hannun Sakataren Zartarwa na Ƙungiyar Mista Clement Isong, ta ce farashin man jiragen sama ya tashi daga Naira 900 a kan kowace lita zuwa Naira 3,300.
A cewar kungiyar, karuwar farashin yana shafar harkokinsu da yau da kullum kuma yana neman durkusar da kasuwancinsu.
A don haka suka bukaci Gwamnatin tarayya tayi duba akan al’amarin domin samar masu da mafita.
You must be logged in to post a comment Login