Connect with us

Labarai

Hukumar REMASAB ta hukunta First Bank da Rufaidah Yoghurt da karin wuraren kasuwanci 5

Published

on

Kotun Tafi-da-gidanka ta Hukumar Kwashe Shara ta Kano REMASAB, ta hukunta reshen First Bank, Rufaidah Yoghurt da wasu wuraren kasuwanci biyar kan karya dokokin tsaftar muhalli.

 

Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar,  Abubakar Ahmad Durumin Iya , ya fitar a Daren jiya Talata.

 

 

Sanarwar ta ce, Mai Shariʼa Halima A. B. Wali ce ta jagoranci zaman kotun, yayin da Lauya Bahijja H. Ali ta gabatar da ƙarar a madadin Hukumar. 

 

Kotun ta hukunta Gidan Man Fara-Fara kan rashin tsafta, yawaitar ciyayi, zubar da shara barkatai da rashin kwandon shara. 

 

Haka zalika Kotun ta hukunta Rufaidah Yoghurt da kantin The King of Smoking kan zubar da shara da sauran laifukan tsafta.

 

Har ila yau, MY Supermarket ya fuskanci hukunci kan rashin tsafta da barin wayoyin lantarki a buɗe, yayin da kotun ta samu Batagarawa Store da laifin sayar da burodi da ruwan roba da wa’adinsu ya ƙare.

 

Reshen First Bank na Titin Murtala Muhammad ya fuskanci hukunci kan rashin tsafta, yawaitar ciyayi da rashin kwandon shara.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!