Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da kafa hukumar samar da tashar lantarki mai zaman kanta

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa hukumar samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta a jihar.
Majalisar ta amince da kafa hukumar ne bayan ta tsallake karatu na uku tare da muhawara kan dokar, wacce za ta bawa kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane damar zuba hannun jari.
Da ya ke yin ƙarin haske kan abinda dokar ta kunsa, shugaban masu rinjaye Lawan Husaini Dala, ya ce hukumar za ta bada damar ƙara habɓaka tattalin arzikin jihar.
Haka kuma majalisar ta karɓi ƙudurin gaggawa kan yawan sace kayan lantarki da ake yi musamman a yankunan karkara.
Ɗan majalisa mai wakiltar Madobi, Sulaiman Mukhtar Ishaq, ne ya buƙaci hakan bayan da wasu ɓata gari suka shiga garin Madobi tare da sace muhimman kayan wuta.
Majalisar dokokin ta Kano, umarci kwamitin ta na harkokin wutar lantarki da ya bincika lamarin tare da gabatar da rahoton sa cikin wata guda.
You must be logged in to post a comment Login