Connect with us

Labarai

PCACC ta kama jami’in gwamnati bisa zarginsa da sace gidan Sauro guda 1,000

Published

on

Hukumar karbar korafi da yaki  cin hanci da rashawa ta jihar kano ta ce ta kama wani mai kula da wajan ajiye kayan gwamnati da ake  zargin da satar gidan sauro guda 1000 da aka tanada don raba wa jama’a. 

 

Shugaban hukumar Kwamared Sa’idu Yahaya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Ya ce tuni suka kama mutumin, kuma bincike ya nuna cewa ya siyar wa da wasu bata gari gidan sauron. 

 

Hukumar ta ce, za ta gurfanar da wanda ake zargin dake aiki a  karamar hukumar Minjibir a gaban kotu sakamakon karkatar da kaddarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!